Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA - ya habarta cewa: dakarun kasar Yemen sun fitar da sanarwar cewa, za su fara kawo cikas a sararin samaniyar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, sakamakon matakin da ta dauka na fadada hare-haren soji a zirin Gaza.
Sanarwar ta ce babban abin da za a mayar da hankali kan wadannan hare-hare shi ne kan filayen jiragen sama na Isra'ila, musamman filin jirgin sama na Ben-Gurion.
Sanarwar ta kuma gargadi kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa da su guji tashi zuwa filayen saukar jiragen sama na Isra'ila tare da daukar gargadin da aka yi da muhimmanci, domin kare lafiyar fasinjoji da jiragensu.
Dakarun kasar Yemen sun jaddada cewa al'ummar kasar Yemen kasa ce mai 'yanci, abar kauna kuma mai cin gashin kanta, kuma ba za ta yi shiru ba wajen tinkarar munanan manufofi da yunkurin tilasta wa kasashen Larabawa, musamman Lebanon da Siriya.
Sanarwar ta ce: "Wannan al'ummar ba ta taba tsoron fuskantar makiya ba, kuma ba za ta mika wuya ba". Allah ne mai taimakonmu, kuma nasara ta al'ummar Yemen ce da dukkan 'yantattun al'ummar musulmi.
Your Comment